26 Agusta 2021 - 10:51
Saudiyya Ta Kirayi Aljeriya Da Morocco Da Su Warware Matsalolinsu Ta Hanyar Tattaunawa

Gwamnatin kasar Saudiyya ta bukaci kasashen Aljeriya da Morocco da su warware matsalolinsu ta hanyar tattaunawa da fahimtar juna.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : A cikin wani bayani da ma’aikatar harkokin wajen kasar Saudiyya ta fitar a yau, ta nuna takaici matuka kan yadda alaka ta yi tsami tsakanin Aljeriya da kuma Morocco, inda lamarin ya kai ga har Aljeriya ta yanke alakarta da kasar Morocco.

Bayanin gwamnatin kasar at Saudiyya ya bukaci dukkanin kasashen biyu da su kai zuciya nesa, kuma su koma teburin tattaunawa domin samun fahimtar juna, domin a cewar bayanin yanke alaka tsakanin kasashe biyu ‘yan juna ba alhairi ba ne gare su da ma dukkanin kasashen larabawa.

Ita ma a nata bangaren kungiyar kasashen larabawa a zaman da ta gudanar a yau, ta fitar da bayani da ke kiran kasashen na Aljeriya da Morocco da su gagauta daukar matakai na warware matsalarsu, kuma kungiyar ta bayyana cewa za ta yi kokarin ganin ta sulhunat kasashen biyu.

A jiya ne gwamnatin kasar Aljeriya ta sanar da yanke alakarta baki daya da kasar Morocco, bayan da ta zargo Morocco da aikata abubuwa da dama na kiyayya da gaba ga kasar Aljeriya, daga ciki kuwa har da zargin cewa Morocco tana da hannu kai tsaye wajen haddasa gobarar daji a cikin kasar ta aljeriya, wadda ta lakume rayukan mutane da dama da kuma jikkata wasu da kuma jawo asarar dukiyoyi masu tarin yawa.

Baya ga haka kuma Aljheriya ta bayyana cewa, kalaman batuncin da ministan harkokin wajen Isra’ila ya yi a kwanakin baya a kasar Morocco a kan Aljeriya, wata alama ce ta cin zarafi ga al’ummar kasar baki daya.

342/